Abubuwa 3 manya da zan gyara kafin in bar ofis – Buhari

Share it:

– Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana wasu abubuwa masu muhimmanci da zai gyara kafin ya bar ofis

– Yayi maganan ne a wani taron kamfanin Shell da akayi a Abuja

Buhari in FEC meeting

Yayin da yake magana da babban daraktan kasa da kasa kuma shugaban kampanin Shell a fadar gwamnati dake Abuja ranar Talata 25 ga Oktoba, ya bayyana abubuwa ukku masu muhimmanci, sune kamar haka:

1. Rikon amana: wajen taron, shugaba Buhari ya bayyana karara aniyarshi ta maido da Najeriya kan hanyar da aka santa a baya na rikon amana. Ya kuma ce zai tabbatar duk mai rike da office zai kasance mai amana ne. Ya kara da cewa wanda yin haka zai karfafa guiwar masu saka jari ya kuma kwantar masu da hankali domin habakar tattalin arzikin kasar.

KU KARANTA: Kashi 43 cikin 100 na yan matan Najeriya na ciki kafin shekara 18 – Majalisar dinkin duniya

2. Neja Delta: A wajen taron kampanin Shell ya nuna damuwars game da tsaron kayayyakin su dake Neja Delta. Shugaban ya tabbatar masu cewa zai yi maganin tsageranci a Neja Delta kafin ya bar ofis.

3. Wutar lantarki: Shugaban ya bada tabbacin gyaran wutar lantarki kafin ya bar ofis. Wannan alkawari yayi dai dai da maganar da yayi cikin Mayu 2016 inda yace wanda a cikin shekaru ukkun da suka rage ma gwamnatin mu, mun daukar ma kanmu alkawarin bada wuta mafi karfin megawatt dubu goma wadda za’a iya rabama jama’a. A cikin 2016 kadai muna da niyyar kara megawatt dubu biyu.

The post Abubuwa 3 manya da zan gyara kafin in bar ofis – Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.