Zaben Edo: Ayi watsi da sakamakon kafafen sadarwa-INEC

Share it:

Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bukaci yan Najeriya dasu yi watsi da sakamako na zaben gwamnna jihar Edo da ake watsawa a kafafen sadarwa.

vllkyt61qhg45vhos.9346d41d

Hukumar tace “mun samu labarin ana yada wasu sakamakon zaben Edo na bogi a kafafen sadardwa na zamani, muna jan hankalin mutane da suyi watsi da wadannan sakamakon, su jira har sai INEC ta fitar da ingantaccen sakamako.

KARANTA:Hanyoyi 6 da Arewa ta tabbatar da karfin mulkinta a Najeriya

Kamar yadda hukumar ta ke cewa jami’an INEC ne kadai zasu iya bayyana sakamakon. Yan takarkaru 19 ne ke neman kujerar gwamnan jihar Edo, sai dai jama’a na ganin wannan zaben bikin gwada kwanji ne tsakanin jam’iyyar APC da PDP.

Jihar Edo na da yawan masu kada kuri’u da suka ka ii,925,105, inda akwai mazabu 192 da rumfunan zabe 2,627. A yanzu dai an kammala zaben a sassa da yawa na jihar.

The post Zaben Edo: Ayi watsi da sakamakon kafafen sadarwa-INEC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.