Obasanjo: Ban ce ka da Buhari ya tsaya takara 2019 ba

Share it:

– Cif Olusegun Obasanjo yace bai ce ka da Shugaba Buhari ya nemi tazarce ba.

– Tsohon Shugaban Kasar yace sharri ne kurum aka yi masa.

– Obasanjo yace ba zai hana kowa tsayawa takara ba.

Obj baba

Cif Olusegun Obasanjo ya musanya cewa ya gargadi Shugaba Muhammadu Buhari da tsayawa takara a shekarar 2019.

Jaridar Vanguard ta rahoto Olusegun Obasanjo yana maida martani game da kalaman da aka ce ya furta na gargadin Shugaba Buhari da tsayawa takara na shekarar 2019. A baya an rahoto cewa tsohon Shugaban Kasar yayi wannan maganar ta bakin wani tsohon Sakataren sa Alex Nwokedi. Sai dai Olusegun Obasanjo yace sharri ne kurum aka yi masa, don bai taba fadan haka ba.

KU KARANTA: Sule Lamdio ya soki tsarin mulkin Shugaba Buhari

Mai magana da yawun bakin tsohon Shugaban Kasar nan Obasanjo, Kehinde Akinyemi ya fitar da wani jawabi Tsohon Shugaban Kasar bait aba furta wadancan kalamai ba. Ya dai bada wannan bayani ne a Ranar Lahadi, 4 ga watan Satumban nan. Ya kuma bayyana cewa na fi shekara uku Obasanjo bai yi magana da tsohon Sakataren na sa ba, kuma har ace yayi wancar magana.

Cif Olusegun Obasanjo yace wannan labari karya ce kuma sharri ne, Cif Olusegun Obasanjo yace ba zai hana Muhammadu Buhari tsayawa takara ba a shekarar 2019. Tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo yace damukaradiyya ta ba kowa damar tsayawa takara, ya rage na jama’a, ko su zaba ko kar su zaba. Obasanjo yace ko ‘ya ‘yan sa bai isa ya hana su tsayawa takara ba, don kuwa suna da dama da wannan ‘yancin a doka.

Cif Olusegun Obasanjo yayi suka game da wannan labari, ya kuma ce rabon da ya hadu da tsohin sakataren na sa yau fiye da shekaru uku, to akan me kuma za a jingina maganar sa gare shi?

The post Obasanjo: Ban ce ka da Buhari ya tsaya takara 2019 ba appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.