Melaye yace Buhari ya sallami Ministocin Tattali da Gwamnan CBN

Share it:

– Sanata Dino Melaye yayi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya dauki matakin gaggawa game da sha’anin tattalin arzikin Kasar nan

– Melaye wanda yake Shugaban Kwamitin Birnin Tarayya a Majalisar Dattawar Kasar yace Buhari ya sallami Ministan Kudi Kemi Adeosun, da kuma Ministan kasafin Kasar Sen. Udo Udoma da kuma Gwamnan Babban bakin Kasar (CBN) Godwin Emefiele

– Wani dan siyasa dan jihar Kogi yace wadannan mutane ba su san aikin su ba

chat-Senator-Dino-Melaye

Sanata Dino Melaye yace ya zama dole Shugaba Buhari ya sallami Ministan Kudin Kasar nan, Kemi Adeosun, da kuma Ministan kasafi na Kasar Sen. Udo Udoma da kuma Gwamnan Babban bakin Kasar (CBN) Godwin Emefiele.

Sanata Dino Melaye, mai wakiltar mazabar Yammacin Kogi yayi kira ga Shugaban Kasa da ya tsige Ministocin sa biyu da kuma Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele. Melaye yayi wannan magana ne Ranar Lahadi a Garin Abuja, inda yace dole Buhari yayi tankada da rairaye cikin Gwamnatin na sa, a cewar Melaye Ministocin ba za su yi iya aikin su ba.

KU KARANTA: Wani tsohon Gwamnan PDP ya soki gwamnatin Buhari

Sanata Melaye yace Buhari kar yayi wata-wata, ya tsige Kemi Adeosun, da Udo Udoma da kuma Godwin Emefiele na Babban bankin Kasar, idan kuwa ana so a farfado da tattalin arzikin Kasar nan. Melaye yace ta tabbata wadannan mutane ba su san aikin su ba, kuma an daina tsoron Shugaban Kasar. Haka kuma dai Sanata Melaye na Jam’iyyar APC ya soki Mataimakin Shugaban Kasar Yemi Osibanjo, wanda shi ke kula da harkar tattalin arzikin Kasar.

Melaye yace babu shakka Udoma Udo Udoma kwararren lauya ne, kuma mutumin kirki, sai da fa aikin kula da kasafin kudin kasa da tsare-tsare ya wuce nan. Sanatan kuma ya bayyana cewa abin da ya faru na Dasuki-Gate ya bayyana cewa Gwamnan Babban Bankin Kasar bai san me ya ke yi ba, kuma shi ke da hannu wajen fadowar darajar Naira.

 

The post Melaye yace Buhari ya sallami Ministocin Tattali da Gwamnan CBN appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.