Shugaba Buhari ya hana raba kyaututtuka wajen taro

Share it:

 

– Gwamnatin Muhammadu Buhari ta haramta sayan kaya ana rabawa wajen taro.

–A baya dai, ma’aikatu sun saba sayen jakunkuna da riguna domin rabawa wadanda suke hallartar taron.

– Gwamnatin Tarayyar ta bayyana cewa wannan na cikin matakan da ake bi wajen rage kashe-kashen kudi a wannan Gwamnati.

Buhari

 

 

 

 

 

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta haramta raba kyaututtukan jakunkuna da riguna da dai sauran su bayan taro kamar yadda dai aka saba a baya. Al’adar da aka saba it ace bayan ko wani babban taro ko kuma karon kara wa juna sani, ma’aikatu da sasan Gwamnati suna sayen kaya irin su, Jaka, da yan Kananan Riguna ana rabawa ga mahalarta. Daga yanzu dai Gwamnatin Muhammadu Buhari ta hana irin wannan, wannan bayani ya zo ne daga karkashin Ma’aikatar kudin Kasar. Salisu Dambatta, wanda shine Darektan yada labarai na ma’aikatar ya bada wannan sanarwar a Jiya Lahadu 31 ga watan Yuli a Abuja. Sanarwar ta bayyana cewa Shugaba buhari ya amince da hakan ne bayan shawarar da Bangaren da ke kula da rage kashe-kashen kudi na kasar ya ba da.

KU KARANTA: AN DUBA SHEKARAR BUHARI NA FARKO

An dai dauki wannan mataki ne ganin cewa Kasar na cikin wani mawuyacin hali, dole ya zama a rage barna da kashe-kashen banza mara amfani. Ga dai cikakkiyar sanarwar:

“Wannan zai sa a samu kudin yi ma Kasa aiki; kamar su harkar kiwon lafiya da ilmi, wannan ne zai fi taimakawa mutanenn Kasa, kuma hakan zai kawo gyaruwar tattalin arzikin Kasa.” Har wa yau dai Gwamnatin Kasar ta Muhammadu Buhari ta bada umarnin da zai sa a rage kashe kudi wajen buga takardun gayyata da sauran su. Gwamnatin Tarayyar ta bada umarni a rika fitar da takardun ne masu launin baki da fari (hakan zai sa a rage cin tawadar fitar da takardun), kuma dai an bada umarnin cewa ka da takardun su rika wuce shafi guda. Game da kasidu kuwa, an bada umarnin ka da a rika cika su da surutu, a rubuta kadai abin da aka fi bukata a ciki. An bada umarnin kuma a rika buga wadannan sanarwa a shafin yanar gizon maimakon barnar takardu a banza, wanda bas a da amfani ga al’umma.

 

The post Shugaba Buhari ya hana raba kyaututtuka wajen taro appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.