Karanta Labarin Muloniya mai sayar da kaji

Share it:

Labarin yadda wani mutum da ya zama muloniya ta hanyar sayar da kaji bayan ya kwashe shekaru yana wasu sana’oi abin karfafa gwiwa ne musammman ga matasa

fried

Tarihin rayuwar Hartland Sanders da yadda ya zama attajiri na cike da darasi, domin Sanders wanda aka sani da Kanar Sanders ya rasa mahaifinsa yana dan shekara 20 da haihuwa, ya kuma yi aure sun kuma rabu da matar, sannan kuma ya rasa dansa a kusan lokaci guda, amma bai yanke kauna ba.

Sanders ya shiga aikin soja a inda ya kai mukamin Kanar amma cikin kunci da rashin yalwa, bayan yayi ritiya, takaicin rayuwa ta sa Sanders ya yanke shawarar hallaka kansa, amma a lokacin da ya samu kudin gratutinsa na ‘yan Daloli, sai ya canza shawara.

KU KARANTA: Direba ya haddasa cunkoso saboda Sallah

Shawarar da ya dauka wacce ta kuma ta sauya rayuwarsa, kuma tushen arzikinsa, ita ce tunanin abin da ya fi iyawa a rayuwarsa, a nan ya gano cewa, a duk shekarunsa na haihuwa babu abin da ya ke yi, ake kuma yaba masa irin yadda ya ke yiwa kaza wani gashi na musamman, wanda ko a aikinsa na soja da wannan ya yi suna.

Da wannan tunanin ya ranci wasu karin kudi kalilan ya kuma hada da nasa ‘yan kadan, ya kuma soma gasa kaza irin tasa, Sanders ya rika bi gida-gida yana sayarwa ya na dan shekara 65, da wannan Sanders ya zama Muloniya bayan ya kafa katafaren gidan cin abinci na KFC wanda ya yi suna a duniya.

The post Karanta Labarin Muloniya mai sayar da kaji appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.