Atiku ya maida martani kan kwace mulkin Buhari

Share it:

-Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya karyata rahoton dake zargin cewa ya samar da wata sabon jam’iyyar siyasa tare da Gwamna Mimiko wanda zai nemi shugabancin kasa na shekara 2019 a karkashinta

-Atiku yace wannan rahoton aikin yan addawa ne wanda suke kokarin kirkiran makirci

-Tsohon shugaban kasar yace shi har yanzu yana biyayya ga Buhari da kuma jam’iyyar APC

makircin

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya maida martani ga rahoton da akeyi cewa shi da Gwamna Olusegun Mimiko na jihar Ondo sun samar da wata kungiya domin su kwace mulki daga jam’iyya mai ci wato jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben shugabancin kasa na shekara 2019.

A wata sanarwa daga mai bashi shawara a harkan labarai, Paul Ibe, Atiku yace rahoton aikin yan adawar sa ne wanda suke kokarin ganin sun haddasa fitina.

KU KARANTA KUMA: Gwamnoni ne suka tursasa Jonathan – Lemo

Atiku ya bayyana cewa an kirkiri rahoton domin a samar da kiyayya tsakaninsa da shugaban kasa Buhari, a dayan bangaren kuma da shugabannin jam’iyyar APC, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Sanarwan ta kuma bayyana cewa duk da dumbin makircin karya da ake yadawa, ba zai shafi biyyayan Atiku ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma shugabncin APC ko kadan ba.

A cewar Ibe, Atiku “ya so yayi shiru game da rahoton karyan, amma ya zabi mai da martani ne saboda karda a dauki shirun sa a matsayin ya yarda da makircin da aka buga a kan shi.”

 

The post Atiku ya maida martani kan kwace mulkin Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.