Yan Najeriya sun maganta da nade-naden Buhari

Share it:

 Yan Najeriya masu amfani da shafukan sada zumunta sun maganta akan nade-naden gwamnatin Shugaban kasa Buhari

Shugaban kasan Najeriya Buhari

Shugaban kasan Najeriya Buhari

Yan Najeriya masu amfani da shafukan sada zumunta sun maganta akan nade-naden shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Wasu yan Najeriya sun zargi suaban kasa Muhammadu Buhari da nada Hausawa musulmai kawai a cikin gwamnatin shi. Sun nuna bacin ransu akan yaddaake canza wasu mutane na wasu kabilu na yankunan Najeriya yake sanya Hausawa.

KU KARANTA: Shugaban hukumar Fursin yayi karyar shekarun aiki

Wannan yazo ne bayan da ya cire Ibe Kachikwu, karamin Ministan Mai daga shugabancin kamfanin Man Najeriya, ya nada Maikanti Baru a matsayin sabon shugaban kamfanin.

Wasu kuma naganin cewa shugaban kasa Muhammadu  uhari yana duba mutane masu hazaka ne domin ya tabbatar da cewa zasu iya yin aikin daya kamata domin ya cika alkwawurran da yayi ma mutanen kasar nan a lokacin yakin neman zabe na 2015.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Fastocin cocin na jihohin Arewacin Najeriya a shekaran jiya. A taron ne shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa wasu daga cikin wadanda suka saci kudaden makamai sun fara nadama akan abubuwan da suka aikata.

 

The post Yan Najeriya sun maganta da nade-naden Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.