Thibaut Courtois yace zai bar Kulob din Chelsea

Share it:

– Mai tsare da gidan Kungiyar Chelsea, Courtois zai bar Kulob din a nan gaba.

 – Golan dai ya buga wasa a Kungiyar Kwallo na Kasar Spain, Atletico Madrid har na shekaru 3.

 – Golan na Chelsea ya tattauna game da zaman sa a Kulob din.

 Kamar dai yadda Thibaut Courtois, dan wasa mai tsaron ragar Kulob din Chelsea yake fada da bakin Sa, Zai bar Kungiyar Kwallon Kafar wanda ke Birnin Landan a nan gaba.

 

Courtoius

 

 

 

 

Dan Wasan, dan Kasar Belgium Thibaut Courtois ya dawo Kulob din Chelsea na Ingila ne bayan ya shafe shekaru 3 a Kasar Spain, inda Kulob din Atletico Madrid ta dauki aron Sa. Dan wasan dai mai shekaru 24 a duniya, ya ci kofin gasar ‘La-liga’ na Kasar Spain da kuma kofin ‘Premier League’ na Kasar Ingila, a rayuwar Sa.

Sai dai Golan na Kungiyar Chelsea, ya kara bayyana cewa yana da niyyar barin Gidan wasa na Stamford Bridge dake Birnin Landan a wani lokaci nan gaba. Thibaut Courtois na cewa: “Abin dai da wuyar furtawa, amma dai bana sa ran zan kare Shekarun buga kwallo na a nan (Yana nufin Kulob din Chelsea)”

A baya dai dan wasan cikin ragar ya taba cewa: “Ni dan Chelsea ne. Idan wani Kulob din Turai na so ya saye ni, sai su yi ma Kungiyar Chelsea magana. Kungiyar ta Chelsea ce ke mallake da ni, su za su duba su gani. Komai sai ya bi ta karkashin su… Idan wasu sun nuna suna son su saye ni, sai Kungiyar ta duba ta gani, Idan Kulob din Chelsea na bukatar in tafi, sai in tashi”. Wannan a baya kenan da yake wani bayani.

The post Thibaut Courtois yace zai bar Kulob din Chelsea appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.