Sojin Najeriya ta musanta zargin da aka yi wa Buratai

Share it:

– Rundunar Sojin Najeriya ta Karyata zargin da aka yi ma iyalin Shugaban Hafsun sojin, Laftana-Janar Buratai na mallakar kadarori a birnin Dubai.

 – A ranar Juma’a, 24 ga watan Yuni aka yada labarin cewa Janar Buratai da matan sa sun mallaki wani gida a Birnin Dubai na Kasar Larabawa.

 – Kwanal KukaSheka Usman Sani, darektan yada labarai na Sojin Najeriya shi ya musanta wannan zargin da ake yi ma mai sojojin Najeriyan.

Buratai

 

 

 

 

 

 

 

 

Wasu bayanai da ke zuwa daga kafar ‘Premium Times’ sun nuna cewa ba shakka, Janar Buratai yana da wasu kadarori a Dubai, wanda ya mallaka daf da ya zama Shugaban Hafsun Sojojin Kasan Najeriyar. Sai dai Sojan Kasar sun karyata zargin mallakar gida da shi da matansa 2. Jaridar ta fahimci cewa, Laftana-Janar Buratai ya nuna abin da ya mallaka lokacin da aka nada sa Shugaban Sojojin Kasa. Rundunar sojin dai sun bayyana cewa Buratai din ya sayi gidan na Dubai ne da albashin Sa da ya tara, shekaru 3 da suka wuce.

Kwanal S.K Usman yace: Buratai ya zayyana wannan gida da sauran duk abin da ya mallaka tun sa’ilin da ya samu matsayin kwamandan rundunar sojojin hadin gwiwa da kuma mukamin Shugaban Sojojin Kasan Najeriyar. ShekaKuka ya bayyana cewa Buratai ba sa da wani akau da bankin ‘Skye Bank’. Kuma ba a taba samun Janar Buratai din ba cikin wata badakala. Jaridar Sahara Reporters ce dai ta buga cewa Janar Buratai da matan Sa, sun mallaki gidaje a Birnin Dubai.

 

Darektan watsa labaran Sojin Najeriyan, Kwanal S.K. Usman yace ba tun yau aka fara kokarin a bata sunan Shugaban Hafsun sojin Kasar ba, a watan Maris na shekarar nan, wasu wai ‘Concerned Citizens’ sun yi kokarin yada irin wadannan Karyayyaki. Ko a farkon wannan makon, wata kafar The Cable ta rahoto cewa an kyale sojojin da suka raunata cikin aiki babu kulawa, wannan ma ba gaskiya bane, Inji Darektan. Kwanal KukaSheka yake karawa da cewa, maganar wai ace Janar Buratai yayi aiki a matsayin Darakta na bangaren samar da makamai na Kasar, karyar banza ce, maras asali. Tun farko ma Janar Buratai mai yi aiki a hedikwatar soji ba a shekarar 2013. Karshen ta ma dai babu wani bangare mai suna ‘Directorate of Procurement’ wancan lokaci, sai shekarar bara aka kafa ta bayan lokacin da Laftana-Janar Buratai ya zama Shugaban Sojojin Kasan Najeriya. Kwanal Kukasheka ya rufe jawabin Sa.

 

The post Sojin Najeriya ta musanta zargin da aka yi wa Buratai appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.