Nasiru El-Rufai ya shirya yaki da masu fyade a Jihar Kaduna

Share it:

– Kwanaki kadan da kama wani rikakken mai fyade a Jihar Kaduna, Gwamna Nasiru El-Rufai ya bayyana bacin ran sa game da wannan mummunan laifi.

 – Gwamna El-Rufai yace za su shiga Kafar wondo daya da duk wanda aka kama yana aikata wannan laifi.

 – Gwamnan yayi alkawarin kare lafiyar wanda duk ya fallasa masu irin wannan aiki.

elrufai declares

 

 

 

 

 

 

 

Nasir El-Rufai ya bayyana tsananin bacin ran sa game da matsalolin fyade da ake fama da shi a Jihar Kaduna cikin ‘Yan kwanakin nan na baya-baya. Jaridar Vanguard ta rahoto Gwamna El-Rufai yana mai nuna matukar bacin rai game da wannan barna, a ranar Jumu’a 24 ga wannan wata, bayan da aka gurfanar da wani Haruna Tukur wanda gawurtaccen mai fyade ne a gaban babban kotun Jihar.

An dai kama matsahin ne dan kimanin shekaru 24 bayan yayi amfani da wata yarinya da bata wuce Shekaru 5 ba a duniya a Unguwar Malali watanni 4 da suka wuce. An dai saba kama Haruna da irin wannan laifuffuka, sai dai a koyaushe yana tsere ma Shari’a. Ana cewa an saba damke Haruna, sai dai kotu ta bada belin Sa, bayan lokaci kadan kuma ‘Yan sanda su kara kama sa da irin wannan laifi.

Mai magana da bakin Gwamna El-Rufai, Samuel Aruwan yana fada ma manema labarai cewa Kotu za ta hukunta Haruna da sauran iri-iren Sa. Aruwan ya bayyana cewa Gwamna El-Rufai zai yi kokarin kare kananan yara da sauran wadanda abin ke aukuwa gare su. Yake kira ga duk wani wanda yake da masaniya game da wani mai fyade da ya hanzarta kai karar Sa.

Haka a dai Jihar Legas na Najeriyar an samu karan fyade sama da 4,000 a cikin shekara guda. Kwamishinan Shari’a na Jihar Adeniji Kazeem ya bayyana cewa, kawo yanzu haka akwai kara kusan 100 da ke gaban Kotu a Jihar.

 

The post Nasiru El-Rufai ya shirya yaki da masu fyade a Jihar Kaduna appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.