Najeriya na iya shiga matsala dalilin Matakin ‘BREXIT’- Utomi

Share it:

– Mutanen Kasar Birtaniya sun zabi Kasar tasu ta bar Kungiyar Turai ta ‘EU’.

 – Sakamakon zaben ya nuna Kashi 52% na Kasar sun zabi su fice daga Kungiyar ta ‘EU’ yayin da sauran Kashi 48% suka zabi da suyi zaman su cikin Kungiyar.

 – Wasu masana tattali a Najeriya suna ganin cewa wannan abu zai jefa Kasar ta Najeriya cikin matsala.

 pat-utomi

 

 

 

 

 

Mashahurin Farfesan nan na Tattali, Pat Utomi yace sauran Kasashen duniya musamman a Afrika za su fara Kokarin bangarewa kamar dai yadda Kasar Birtaniya tayi. Utomi yake cewa, yana ji cewa kasashe da dama za su fara tunanin ficewa daga Kungiyoyin Su. A cewar Sa, Kasar Sierra Leone ko Najeriya na iya biyo sahu. Farfesa Utomi yake cewa an wuce zamanin da Kasashe za suyi ta zama a cikin Kungiyoyin da ba su bukata, yana mai bayyana hakan a matsayin wani bauta.

 Farfesan tattalin arzikin, Utomi yana cewa: “Kungiyar EU za tayi kokarin kulla sabuwar alaka da sauran Kasashe, yayin da ita kuma Birtaniya za tayi kokarin rike dangantakar ta da sauran Kasashen duniya kamar su Najeriya.”

Shi kuma wani Farfesa mai suna Bola Akinterinwa, cewa yake, ‘Yan gudun Hijiran Najeriya sai su shirya shiga wani hali a nan gaba dalilin fitar Birtaniya daga EU. Yake cewa wanda suka zabi ficewar ta Birtaniya suna ganin laifin wadanda suka je ci-rani a Kasar su wajen matsalolin da Kasar ke fuskanta, kama da rashin aikin yi, rushewar tattali, hada ma har da cunkoso bisa titi. Wani Farfesa kuma mai suna Adenikinju Adeola, ya bayyana cewa wannan mataki zai kawo durkushewar tattalin Arzikin Najeriya, ta wajen sayen man Kasar, wanda ta nan aka dogara. Wani babban lauya na Kasar, Tayo Oyetibo (SAN) yace idan dai Kasar Birtaniya, wacce ta ke da babban kawance da Najeriya za ta fice daga Kungiyar EU, za ku gane cewa lallai wannan na da matukar tasiri ga Kasar ta Najeriya.

Yayin da kowa ke tofa albarkacin bakin Sa game da ficewar Birtaniyan daga Kungiyar EU, Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari yana mai cewa: “Ajiye mulki da Shugaba Cameron yayi, ya nuna cewa ya cika mai son damukoradiyya, wanda ya san ‘yancin jama’a.”

 

 

The post Najeriya na iya shiga matsala dalilin Matakin ‘BREXIT’- Utomi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.