Gareth Bale ya jagoranci kasar shi zuwa Euro2016

Share it:

An fafata tsakanin Kasashen Birtaniyan biyu; Kasar Wales da kuma Kasar Northern Ireland a Gasar Zakarun Nahiyar Turai na Kwallon Kafa. Sai da aka kai minti na 75 ana cangaras, kafin kwatsam dan wasa Gareth Mc Auley ya jefa kwallo cikin ragar Sa. Wannan dai shiyasa Kasar ta Wales tayi nasara kan makwabciyar ta, Northern Ireland da ci daya rak mai ban haushi.

Kasar ta Wales mai dauke da ‘yan wasa irin su: Gareth Bale, Aaron Ramsey da sauran su, ana tunanin ita za tayi nasara tun kafin a take wasa. Sai dai abin bai zo da sauki ba kamar yadda kowa yake tunani. A minti na 58 ne ma mai-tsaron ragar Kasar ta Northern Ireland, Michael McGovernk ya buge wata kwallo da Gareth Bale ya buga. Gareth Bale din dai ya saba cin irin wannan bugu na ‘firikik’. Ko a gasar nan, dan wasan gaban na Real Madrid ya ci irin wannan kwallo a wasan da suka kara da Kasar Ingila inda aka tashi 1-2.

 bale decima

 Duk da Kasar ta Northern Ireland sun yi taurin kai, amma a minti na 75 na agogon wasa, Gareth McAuley ya zunduma kwallo cikin ragar gidan sa. Gareth Bale ne dai ya kwaso kwallon zuwa ga dan Garin Sa Robson-Kanu, inda shi kuma McAuley Gareth kawai ya tura ta cikin ragar sa.

A yanzu dai haka, Kasar Wales tayi nasara inda ita kuma Northern Ireland an kora ta gida. ‘Yan Kwallon Kasar Wales din da ake yi ma lakabi da ‘The Dragons’ za su kara a zagaye na gaba na gasar da duk wanda yayi nasara a wasan da za a buga tsakanin Kasar Hungary da Kasar Belgium daga baya.

The post Gareth Bale ya jagoranci kasar shi zuwa Euro2016 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.