Fani Kayode ya ji a Jikinsa a hannun EFCC

Share it:

Wata majiya ne ta shaida cewa a ranar 26 na watan Yuni neTsohon minstan Jirage, Femi-Fani Kayode ya ji ajikin sa hannun wani Jam’in EFCC. Majiyar ta fadi cewa an ci ma Fani Kayode da wasu da ke rike a EFCC din a dalilin irin Ibadar da suke yi.

 

Fani Kayode

Fani Kayode

 

Labarin day a ishe mu tabbatar mana da cewa an ci ma Fani Kayode a ofishin EFCC tare da wasu tsararrun Mutane, in da ake zargin wani Jami’in EFCC din Suleiman Kabiru da yi, a ranar 26 ga watan Yuni. Majiyar ta kara da cewa dama shi Jami’I Suleiman Kabiru ya dade da yake matsa ma Mutanen da ke tsare a hannun hukumar a yayin da suke gabatar da Ibadar su. “Matsin ya kai makura ne a ranar Asabar in da Jami’I Sulaiman wanda dan Kebbi ne ya far ma Fani Kayode a lokacin da yake Ibadar sa ba tare da tsokana ba, wanda hakan yayi sanadiyyar ji Mai Ciwo.”

Majiyar ta kara da cewa Jami’I Sulaiman ya nuna bacin ransa sosai da har ma yake tambayar Fani Kayode da menene yasa ba zai bi umarnin sa ba. Sa’anan ta kara da cewa amma wasu daga cikin sauran Jami’an da ke wurin sun yi kokarin hana shi don kada ya kara ji mai wasu raunukan.

Har zuwa yanzu da muke hada muku wannan labarin, mai magan da yawun EFCC Wilson Uwujaren bai amsa binciken da muka fara akan harin. Shi dai Fani Kayode an kama shi ne bayan ya amsa gayyatar da EFCC ta masa ne a ranar 9 ga watan May. A cikin sakon  gayyatar, EFFC t ace tana binciken zargin Almundahana ne da rashawa a kan wata kamfani mai suna ‘Joint Trust Dimension Limited’ da keda alaka da Fani Kayode.

Hukumar ta kara zata gurfanar da Tsohon Ministan tare da wasu Mutane guda 2 a Kotun Tarayya da ke Ikoyi a garin Legas akan zargin sa da aikata laifuka guda 17 wadanda suka danganci Almundahana da satar kudi. Sai dai har sau biyu Alkalan da zasu saurari karan ba su samu daman zuwa kotun ba, su ko dangin Fani Kayode suna zargin Alkali Hassan Sule da kawo cikas ga gurfanar ne don ya tsawaita ma Fani Kayode zama a Gidan kaso.

The post Fani Kayode ya ji a Jikinsa a hannun EFCC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.