Buhari yayi Magana akan murabus din David Cameron

Share it:

-Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi magana akan murabus din da firam Ministan Birtaniya, David Cameron yayi.

-Wannan ya nuna karfin zuciyan sa na yarda da abin da jama’a suka zaba.

 Shugaban kasa Muhammad Buhari ya yabi karfin zuciya da kishin kasan David Cameron, na yanke shawaran murabus da kujeran sa a matsayin Firam Ministan Birtaniya bayan shekaru 6 a kai saboda zaben da yan birtaniya suka yi na barin kungiyar turawa.

david-cameron-global-economy

A wani jawabin da mai magana da yawun Shugaban kasa, Garba Shehu , ya bayar, buhar yace ” bai ji dadin murabus din da david Cameron yayi ba , wanda zai fara a watan oktoba.” Shugaba buhari yace yaji dadin zama da goyon bayan da fahimta da firam ministan ya bashi shekarun da suka gabata.

Shugaban kasa yace : “Murabus din da David Cameron yayi na sakamakon zaben da mutanen Birtaniya suke yi na fita daga kungiyar turawa ya nuna karfin zuciyan Shugaban da ya yarda da maganan mutanensa, ko bai gamsu da yankewarsu ba”.

KU KARANTA: Ga wani manyan shugaban kasar da Shugaba Buhari ya maraba a Abuja (hotuna

Shugaba buhari yace , gabatar da ra’ayin mutane kafin ra’ayin sa, ya nuna cewa firam ministan birtaniya shugaban demokradiya na kwarai ne.Shugaban kasa Muhammad buhari yace yana sa ran najeriya zata cigaba da hadin kanta da goyon baya tsakinin ta da birtaniya.

The post Buhari yayi Magana akan murabus din David Cameron appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.