Kungiyar Kwadago zata cigaba da tattaunawa da Gwamnati

Share it:

– Kungiyar kwadago da Gwamnatin tarayyar Najeriya zasu cigaba da tattaunawa akan karin farshin Mai da aka samu a najeriya

– Kungiyar ta janye yajin aikin nata ne a ranar lahadi domin ta tattauna da Gwamnati akan karuwar farashin man

– Kungiyar ta gudanar da zanga zanga na kwanki 3 a makon daya wuce

nlc

Yan kungiyar kwadago

Gwamnatin Najeriya da kungiyar Kwadago ta najeriya zasu fara tattaunawa da nufin shawo kan karain farashin Mai da aka samu a Najeriya da kuma yajin aikin da kungiyar ta shiga na kwanki 3.

Sakatare mai kula dalabarai na ma’aikatar kwadago ya bayyana ma yan Jarida cewa, a yau 25 ga watan mayu da misalin karfe 2 na rana sashen gwamnati da wakilan kungiyar kwadago zasu tattauna akan batun a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya a birnin Abuja.

A makon daya wuce ne kungiyar Kwadagon ta tattauna da Bola Tinubu wanda ya shawarce su su janye yajin aikin. taron nasu yazo ne bayan da Ministar Kwadago, Chrris ngige ya bayyana cewa Gwamnati baza ta tattauna da kowa ba sai sun janye yajin aikin nasu.

An jinkirta taron Gwamnati da kungiyar Kwadago ne saboda kungiyar manyan ma’aikatan Mai da isakan gas (PENGASSAN), sun bawa gwamnati sanarwar shiga yajin aikin su a mako mai zuwa.

Jami’in labarai na ma;aikatar kwadago Olowookore ya bayyana cewa amma sa bakin Ministan Kwadago da kuma karamin Ministan Mai ya sanya yan kungiyar suka fasa shiga yajin aikin.

Karamin Ministan mai ya bayyana ma ma’aikatan da dukkanin masu ruwa da tsaki a ciki JVCC cewa zasu samu labari mai kyau kafin taron da zasuyi nan gaba a watan Yuni.

Ministan ya bayyana cewa da akawai kwamiti wanda yake karkashin Karamin Ministan Kwadago, James Ocholi wanda ya mutu. Amma saboda muhimmancin abun shi zaya zama shugaban kwamitin a watan Yuni domin kawo karshen abun.

A wani labarin kuma, karin mai da gwamnati tayi bai yima Farfesa Tom David West dadi ba. Farfesa Wanda tsohon Ministan Mai ne ya bayyana cewa abunda gwamnatin Tarayya tayi na karin kudin Mai bai kamata ba.

 

The post Kungiyar Kwadago zata cigaba da tattaunawa da Gwamnati appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers | Read on NAIJ.COM.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.