Farin jinin Buhari ya ragu sosai – Bincike

Share it:

– Farin jinin shugaban kas Muhammadu B uhari ya ragu sosai

– A watan Aktoba kimanin kaashi 80 na mutanen Najeriya na goyon bayan shi

– Yanzu ya koma kasa da kashi 42

buhari infographics

Wani bincike da kungiyar NOI ta gudanar ya nuna cewa farin jinin shigaban kasa Muhammadu Buhari ya ragu inda a cikin shekara 1 ya rasa magoya baya da yawa.

KU KARANTA: 

Binciken ya nuna cewa kashi 16 na wadanda suka amsa amsa tambayoyin basu yanke shawara ba. Wannan ke nuna canjin ra’ayi na kashi 6 daga cikin su. An gudanar da binciken ne ta hanyar tambayar jinsi daban-daban, wuraren da mutane suke zama da kuma abubuwa daban-daban akan tattalin arziki, tsaro da sauran su.

A watan Junairu daya wuce, farin jinin shugaban kasar yana a kashi 69, a watan Fabrairu amincewar yan Najeriya a game da gwamnatin nashi sai ya koma kashi 55, a watan Marsin kuwa, sai ya dawo kashi 47, inda a watan Afrillu yake a kashi 42.

Daga cikin manyan abubuwan da ake tsammanin suke sanya farin jinin shugaban kasar ke ragewa sun hada da;

1. Rashin wutar lantarki

2. Rashin albarkatun Man fetur

3. Tsadar Mai

4. Faduwar darajar naira

5. Ziyarar da yake yi kasashen waje

6. Hare-haren Fulani

7. Tsageranci a Nija Delta

8. karin kudin wutar lantarki

Amma da yawa daga cikin yan Najeriya sun yaba ma shugaban kasa Muhammadu Buhari sosai musamman akan sha’anin tsaro. Daga hawan shugaban kasa Buhari zuwa yanzu sojojin Najeriya sun samu nasarori sosai akan kungiyar Boko Haram inda suka kashe Kwmandojin kungiyar kuma suka kama dayawa daga cikin su.

Haka zalika, da yawa daga cikin yan Najeriya sun yaba ma shugaban akan yadda yake yaki da rashawa da cin hanci a kasar. Sun bayyana cewa suna kyautata zaton za’a ci nasara.

Idan zaku iya tunawa, a wannan watan ne Firayim Ministan kasar Ingila ya bayyana cewa najeriya da kasar Afghanistan ne suka fi kowanne rashawa a duniya. Wannan ya sanya ya samu martani daga shugaban kasa Buhari da al’ummar Najeriya.

The post Farin jinin Buhari ya ragu sosai – Bincike appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers | Read on NAIJ.COM.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.