Yan Najeriya, mutane suke butulce da ni’mar Allah ne – Bashir Abdullahi El-Bash

Share it:

– Wani mutum mai suna Bashir Abdullahi El-Bash ya rubuto akan jaridar Rariya tunaninshi da yan Najeriya da Najeriya

– Shekara daya da ya wuce Najeriya musamman ta Arewa tana cikin halin zubar da jini da dashe jama’a da ba su ji ba su gani ba.

– Idan ka fita kasuwa cikin tsoro kake, haka idan ka shiga tashar mota, ‘yan makaranta suna bacci da dare a zo a yanka fiye da 50, mun shekara kusan biyar a cikin wannan bala’i da busibar.

Ku karanta kamar yadda El-Bash ya rubuta takardarshi cewa, mu, mutanen Arewa, mun koma ba kowa ba a Najeriya matar tsohon shugaba, Dakta Goodluck Jonathan ta zage mu, Tompolo ya za gemu, Dokubo Asari ya zage mu, ana yi wa sojojin mu ritaya ba bisa ka’ida ba. Yan Nija Delta sun tada bam a Abuja, Jonathan ya fito yace mutanen Arewa ne.

 KU KARANTA KUMA:

Muna cikin wannan bala’in zabe ya zo muka koma ga Allah muka yi kuka muka roke shi da ya fitar da mu daga wannan halin, Allah ya ji tausayin mu ya kawar da gwamnatin da muke ganin ba ta yi mana adalci, ya Kawo mana mutum wanda ko makiyansa sun san yana da rikon amana. Cikin shekara daya Allah ya taimakemu mun sami zaman lafiya, mutumin Maiduguri sai ya yi bacci har gari ya waye bai tunanen za’a zo a farma gidansa. Za ka fita kasuwa lafiya, za ka je Masallaci lafiya.

butulce

Yan kungiyar Boko Haram

To ina ganin wannan kadai ya isa mu godewa Allah akansa, sannan mu ci gaba da yi wa gwamnati addu’ar samun nasarar shawo kan tarin matsaloli da kasarmu take ciki.

Sannan game da matsalar man fetur, ya kamata mu san cewa koda Buhari ya zo ya tarar Amsna kashe mu raba a harkar mai, wasu tsirarun mutane suna zaluntar aasa akai,l. To wadannan mutanen da kamfanoni a yanzu Buhari ya taka masu birki akan zaluncin da suke, su kuma mutane ne masu karfin gaske suke rike da tattalin arzikin kasa, saboda haka suka hada kai sai sun ga sun durkusar da gwamnatin Najeriya ta hanyar kawo matsalar mai, sun yi haka ne domin su huce fushin su na hana su kashe mu raba da gwamnati ta yi.

butulce

Mai kasuwan ruwan leda acikin kasuwar Mile 12 a jihar Legas

To zai dauki lokaci kafin gwamnati ta yi nasarar karya wadannan Azzaluman, sannan mu sani wannan gwamnatin tana fama da makiya har a cikin jam’iyyar APC mai mulki, ga yan jam’iyyar PDP a gefe. Duk wani azzalumi a Najeriya babbar fatar sa ita ce talakawa su dawo daga rakiyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin suna ganin hakan zai ba su damar dawowa mulki su ci gaba da gasa mana aya a hannu.

A karshe mu sani Buhari dai dan Adam ne duk yadda yake son al’amari ya gyaru sai da taufiqi daga Allah, tun yana matashi yake fafutuka domin ganin mun sami rayuwa ta gari, da shi aka yi yakin Biafra, ya rika mukamai da dama ba a taba samun sa da satar dukiyar jama’a ba.

To idan muka butulce wa wannan ni’imar, Wallahi Allah zai iya juya mana baya, ya bar mu halayenmu. Allah ka kawo wa kasarmu mafita mafi alkairi, ka magance mana matsalolin da muke fama da su. Amin.

The post Yan Najeriya, mutane suke butulce da ni’mar Allah ne – Bashir Abdullahi El-Bash appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.