Manyan Labarai Guda 10 Da Sukayi Fice A Ranar Litinin

Share it:

Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Litinin 21 ga watan Disamba. Ku duba domin ku same su.

sambo dasuki vii

Kanar Sambo Dasuki

1. Dasuki, Yuguda Sun Samu Beli 
Wata babbar Kotu dake Abuja ta ba Kanar Sambo Dasuki, Bashir Yuguda da sauran mutane da hukumar EFCC take rike dasu Beli. Amma har yanzu suna kurkuku har Sai an cika sharuddan belin.
2. Obasanjo A Gargadi Yan Najeriya Akan Wani Yakin Basasa
Sojin Shugaban kasa Obasanjo ya gargadi yan Najeriya akan sake yin wani yakin basasa. Ya bayyana cewa akwai bukatar a ringa magana ba fada ba.
3. Kudaden Sayen Makamai: EFCC Zata Gayyaci Jonathan
Hukumar EFCC zata gayyaci Tsohon shugaban kasa Jinathan akan kudaden makamai da aka kashe a lokacin shi.
4. Gwamna Wike Ya Dage Da Addua Idan Yana San Komawa Gidan Gwamnati – Mayu
Kungiyar Mayu Ta shawarci Wikebya cigaba da addua Idan dai har yana San ya koma gidan gwamnati
5. Magoya Bayan APC 7000 Dasu Koma PDP A Ondo
Kimanin magoya bayan APC 7000 zasu canza sheka zuwa PDP a jhar Ondo.
6. Takalman Zahra Buhari Sun Jawo Nace Kace
Wasu takalman da Zahra Buhari Ta sanya a lokacin bikin ranar haihuwar ta sun jawo nace kace.
7. Abun Mamaki: Wata Mata Ta Haifi Kunkuru
Wata Mata Mai Suna Cassandra, a karamar Hukumar Ihiala, a JIhar Anambara Ta haifi kunkuru.
8. Yan Boko Haram Sun Tare Hanya, Sun Dana Nakiya
Yan kungiyar Boko Haram sun kulle wasu hanyoyi a jihar Borno, sun dana nakiyoyi domin bana sojoji wucewa.
9. Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Zaben Maman Taraba
Kotun daukaka Kara Ta bayyana cewa Aisha Alhassan ce zababbiyar gwamnan jihar Taraba, ba Darius Ishiaku ba.
10. Arsenal Ta Lallasa Manchester City 2-1
Kungiyar kwallo ta Arsenal, ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta nance Man City bayan da suka amshi bakuncin Manchester City a gidan su, Emirate.

The post Manyan Labarai Guda 10 Da Sukayi Fice A Ranar Litinin appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.

loading...
Share it:

Latest Stories

Post A Comment:

0 comments:

We’re eager to see your comment. However, Please keep in mind that all comments are moderated according to our Comment Policy and all the links are nofollow. Using keywords in the name field area is forbidden.
Comment Using Either Disqus or Default Comment Mode.